Shugabannin Arewacin Najeriya sun nemi a hukunta tsohon Mataimakin Gwaman Babban Bankin Najeriya (CBN) Obadiah Mailafiya kan zargin da ya janye na cewa wani gwamnan yankin ne shugaban Boko Haram.
Ƙungiyar Tuntuba ta Arewa (ACF), ta buƙaci doka ta yi aiki a kan Mailafiya, wanda a lokacin da yake zargin ya haƙiƙance cewa gaskiya yake faɗa har da taƙamar cewa digirinsa na uku a Jami’ar Oxford ya yi.
Sai dai bayan kwanaki ya fito yana bayar da haƙuri da cewa maganganun da ya yi a zargin ya ji su ne a kasuwar ƙauye.
A hirar da aka yi da shi a gidan radiyo Nigeria info wadda ta tayar da ƙura, Mailafiya ya ce Boko Haram da ‘yan bindiga sun hada baki suna shirin tayar da yaƙin basasa a 2022 a Najeriya.
Ya ce jiragensu na ta zirga-zirgar raba makamai da kuɗaɗen da kayan aiki tamkar babu dokar kulle.
Bayan hukumar tsaro ta DSS ta yi masa tambayoyi kan zarge-zargen, Mailafiya a hira da sashen Hausa na BBC ya yi da shi daga baya ya ce ya ji bayanan ne a bakin wasu Fulani a kasuwar ƙauye.
Sakataren Yaɗa Labaran ACF, Emmanuel Yewa ya ce zargin na da razanarwa domin yana maganar “yakin basasa da jiragen jigilar makamai da kudade ne.
“Zargi irin wannan daga mutum kamrsa babban abu ne da ya kamata a dauka da muhimmanci. Amma mun jira mu ga doka ta yi aikinta.
ACF ta buƙaci manyan mutane su rika zurfafa tunani kafin su furta kalamai don kar su tayar da fitina.