Rahotanni daga majiyarmu sun nuna cewa, a karshen makon nan gwamnatin tarayya ta nuna sha’awarta na fara tattaunawa da kungiyar Malaman Jami’o’in Nijeriya wato ASUU domin kawo karshen yajin aikin da kungiyar ta shiga na tsawon wata hudu ke nan zuwa hada wannan rahoto.
Jaridar THISDAY sun labarto cewa; dukkanin bangarorin guda biyu sun yi wani motsi na musamman domin ganin sun dawo kan teburi domin ci gaba da tattaunawa dangane da rashin jituwa da sabanin da suka samu kan tsarin IPPIS a cikin tsarin gudanar da jami’a sakamakon zargin da ake yiwa membobin ASUU da yi wa tsarin zagon kasa.
Kungiyar dai ta ASUU a lokuta da dama ta bayyana cewa ba ta amince da tsarin IPPIS ba, domin a cewarta akwai algus a tsarin, inda suka ce a maimaikon amfani da tsarin IPPIS din, sun samar da na su tsarin na UTAS, inda a halin yanzu suka tabbatar da cewa a shirye suke su bayar da tsarin domin hukumomin gwamnatin tarayya su gwada tsarin na su.
Shugaban ASUU din na kasa, Farfesa Biodun Ogunyemi a karshen makon da ya gabata ya ce sun gana da ministan ilimi, Malam Adamu Adamu inda suka tattauna yadda zai taimaka a dawo da ci gaba da tattauna da gwamnatin tarayya domin bayyana damuwowinsu. Haka zalika ministam kwadago, Dr. Chris Ngige ya tabbatar da cewa a shirye yake ya gayyaci kungiyar domin zama akan teburin sulhu.