Rahotanni na nuni da cewa; a kalla mutum 33 suka rasa rayukansu akasarinsu mata da kananan yara bayan wasu ‘yan bindiga sun kai sabon farmaki a kauyukan yankin Atyap da ke Karamar Hukumar Zangon-Kataf ta jihar Kaduna.
Jaridar Daily Trust ta Najeriya ta labarto cewa, an kaddamar da jerin hare-haren ne da misalin karfe 11 na dare a ranar Laraba da kuma karfe 1 na dare a ranar Alhamis a kauyukan Apyiashyim da Atak’mawai da Kibori da Kurmin Masara da ke karkashin masarautar Atyap a Zangon Kataf.
Wata majiya ta bayyana cewa, an kai farmakin ne a daidai lokacin da ake tafka ruwan sama mai karfin gaske, yayin da tsagerun suka karkashe jama’a tare da raunata wasu da dama duk da cewa akwai dokar hana fita ta tsawon sa’o’i 24.
Daya daga cikin mazauna yankin ya ce, an kai musu farmakin ne a daidai lokacin da al’umma ke barci a gidajensu.
‘Yan bindigar sun shafe tsawon lokaci suna harbi kan mai uwa da wabi, yayin da majiyar rundunar ‘yan sandan jihar Kaduna ke cewa, mutane 21 ne suka rasa rayukansu.