‘Yan bindiga sun yi garkuwa da mutane ashirin a yankin ƙaramar hukumar Shiroroo da ke jihar Neja.
Wannan na zuwa ne awanni kaɗan bayan da wasu ‘yan bindigar suka kai makamancin wannan harin a garin Kagara hedikwatar ƙaramar hukumar Rafi a jihar ta Neja.
Bayanai sun ce ‘yan bindigar sun kai harin ne a ƙauyen Adagbi da ke mazaɓar Galkogo da safiyar yau alhamis.
https://dimokuradiyya.com.ng/an-kama-mai-safarar-makamai-a-jihar-neja/
Shaidun gani da ido sun shaidawa manema labarai cewa, ‘yan bindigar sun shigo ƙauyen ne akan babura tare da yin harbi sama kafin daga bisani su sace mutanen waɗanda akasarinsu mata ne.
Sai dai har ya zuwa yanzu, rundunar ‘yan sandan jihar ta Neja ba ta fitar da sanarwar faruwar lamarin ba.