Ministan lura da yankin Neja Delta, Sanata Akpabio, ya fallasa yadda hukumar NDDC da aka dorawa alhakin raya yankin aka maishe ta na’urar tatsar kudi ga ‘yan siyasa ke wawusar kudin da suke kashewa wajen yakin neman zabe.
Ministan ya bayyana haka ne yayin karbar bakuncin tawagar kungiyar dillalan man fetur ta Nijeriya IPMAN a birnin tarayya Abuja a karshen makon da ya gabata.
Akpabio ya ce matsalolin rashawa da almundahana da babakere sun dade da yi wa hukumar raya yankin ta Neja Delta NDDC, katutu a wuya tsawon akalla shekaru 19, kafin nada shi Ministan lura da yankin a shekarar 2015.
Tsohon gwamnan na Akwa Ibom, ya ce kamata ya yi majalisar dokokin Nijeriya ta fadada binciken da take yi kan laifukan sace kudaden hukumar na tsawon shekaru 19 da kafa ta, a maimakon zarge-zargen almundahanar kudaden daga watan Fabarairu zuwa Yuli na shekarar 2020 da muke.
Ministan lura da yankin ya kara da cewar jimillar naira tiriliyan 5 gwamnati ta bai wa hukumar ta NDDC a tsawon shekaru 19, ba tare da an aiwatar da ayyukan da aka tsara ba.