Tsohon Kakakin Majalisar Wakilai, Yakubu Dogara ya sauya sheka daga Jam’iyyar PDP zuwa jam’iyya mai mulki ta APC.
Bashir Ahmad, mai taimaka wa shugaban ƙasa Muhammadu Buhari kan kafafen sadarwar zamani shi ne ya wallafa hakan a shafinsa na Twitter.
Wadansu bayanai sun tabbatar da cewa; Dogara ya koma APC ne bayan da ya gana da shugaban kasa Muhammadu Buhari a fadar gwamnati dake Abuja.
A yau Juma’a ne dai Yakubu Dogara tare da Gwamnan Yobe Mai Mala Buni suka kai ziyara ga Shugaba Muhammadu Buhari.
Idan mai karatu bai manta ba, a shekarar 2018 Yakubu Dogara tare da wasu ‘yan majalisa suka sauya sheƙa daga APC zuwa jam’iyyar adawa ta PDP.