JARIDAR DIMOKURADIYYA: Rundunar sojin kasar Sudan ta bayyana kama shugaban kasar Sudan Omar al-Bashir, bayan da aka shafe watanni a zanga-zanga a kasar ta Sudan, sannan rundunar ta bayyana soke kundin tsarin mulkin kasar ta Sudan, a sanarwar juyin mulki da rundunar ta bada, inda ta kawo karshen shekaru 30 na mulkin al-Bashir din.
Gwamnatin rikon kwaryan wacce rundunar sojin za ta jagoranta za ta yi riko na tsawon shekaru biyu, inda daga bisani za a gudanar da zabe, sannan za a sanya dokar ta baci na tsawon shekaru uku, har wa yau an saki dukkan fursononin siyasa da gwamnatin al-Bashir din ta garkame, ana kokarin sakin jagororin da suka jagoranci zanga-zangar da ta yi sanadiyyar yiwa al-Bashir din juyin mulki.
Mataimakin shugaban kasar Sudan Awad Ibn Auf shine ya saki wannan sanarwar wacce ake sa ran za ta kawo karshen zanga-zangar da aka shafe watanni hudu ana yi a kasar ta Sudan, inda masu zanga-zangar suke yin Allah-wadai da gwamnatin al-Bashir musamman akan tsadar rayuwa a kasar ta Sudan.
Har yanzu ba a kai ga sanin takamammen matakan da rundunar sojin kasar za ta dauka ba, amma har zuwa lokacin hada wannan rahoton masu zanga-zangar suna kan yin zaman dirshan a hedikwatar sojojin kasar inda suke rera taken “Mun yi Nasara, Ya fadi warwas” wato ma’ana sun yi nasarara korar shugaba Omar al-Bashir.