Dan takarar gwamna a jihar Kogi a jam’iyyar PDP, Musa Wada ya yi watsi da sakamakon zaben da hukumar zabe mai zaman kanta wato INEC ta fitar.
Da yake yiwa manema labarai bayani a garin Lokoja a ranar Lahadi, Musa Wada ya yi zargin cewa sakamakon zaben na boge ne aka fitar domin ayyana Yahaya Bello na APC a matsayin gwamnan jihar.
Har wala yau ya zargi APC da magudin zabe musamman a Kogi ta tsakiya wato inda gwamnan ya fito.
Ya yi alkawarin zuwa kotun sauraren kararrakin zabe domin kalubalantar sakamakon zaben.