A ranar Laraba ne gwamnan jihar Kaduna Malam Nasir El-Rufa’i ya bayyana cewa akwai yiwuwar gwamnatin Kaduna ta sake dawo da dokar kulle a jihar, matukar al’ummar jihar zasu yi burus da dokokin kariyar kai da aka shimfida musu.
“In har muka samu adadin masu dauke da cutar ya karu, to tabbas zamu sake dawo da dokar kullu”. Inji El-Rufa’i.
Gwamnan ya bayyana haka ne a yayin da yake buɗe sabuwar motar gwaji da hukumar USAID ta bai wa jihar a juya Laraba.
“Ina ƙara jan hankalin mutanen Kaduna da sursu fita in har ba dole ta zamo ba, saboda zamu yi dawo da dokar kulle, don ganin mun kare rayukan al’umma”. Cewarsa.
https://dimokuradiyya.com.ng/an-sassauta-dokar-kulle-a-jihar-kaduna/
A yayin da yake jawabi, El-Rufa’i ya kara da cewa motar tana ɗauke da kayan gwaji da dama, kuma an jima da bawa gwamnatin Najeriya daga gwamnatin Amurka ƙarƙashin kulawar hukumar USAID domin yin gwajin cutar tarin TB (tuberculosis).
“Amma da yake muna cikin yanayin annobar Korona, za a cigaba da amfani da ita wajen gwajin ƙwayar cutar, a yanzu haka an yi amfani da ita wajen gwada mutane sama 200 wanda duk am same su da ƙwayar cutar”.
“Motar ana amfani da ita ne wajen ɗaukar samfurin gwajin mutane a anguwaninsu, kuma a yanzu haka akwai wajen kaso 16 na unguwannim da aka gwada na ɗauke da cutar ta Korona”, inji El-Rufa’i.