Ƙungiyar ƙwadago da kare haƙƙin ma’aikata ta ƙasa tace bata ga amfanin mafi ƙarancin albashi ga ma’aikata ba in har gwamantin tarayya zata yi ƙarin kuɗin Mai.
Shugaban ƙungiyar Ayuba Wabba shi ne ya bayyana hakan a yayin tattaunawarsa sa jaridar Punch a ranar Talata, idan yace ya kamata a ce gwamnati ta yi nazarin yanayin da naira take ciki da kuma kuɗin da ake biya na mafi ƙarancin albashi.
Reshen ƙungiyar dake wasu jihohin sun bayyana cewa ƙarin kuɗin Wutar Lantarki ds kuma tashin farashin Mai yasa mafi ƙarancin albashin ba shi da wani tasiri.
Sai dai a ranar Litinin Ministan yaɗa labarai da al’adu Mista Lai Mohammed ya bayyana cewa duk da ƙarin kuɗin Mai da gwamnatin ta yi Najeriya ce mafi ƙarancin kuɗin mai a nahiyar Afirka.
Sai dai Wabba na ganin cewa ƙarin kuɗin ba zai haifar da ɗa mai ido ba domin gwamnati ba ta yi abinda ya dace da kuma lokacin da ya dace ba.