Ƙungiyar Direbobin Mai da Iskar Gas ta ƙasa (NUPENG) ta umarci direbobin tankokin mai da su fara yajin aiki daga safiyar Litinin a jihar Legas.
Shugaban ƙungiyar ta NUPENG shiyyar Kudu maso Yamma Tayo Aboyeji ya ce ƙungiyar rashin cimma matsaya a tattaunawarsu da gwamnatin jihar a ranar Lahadi ya tilasta su shiga yajin aikin.
Ya ce, “Sai dai kawai muka ce za mu tsunduma yajin aiki sannan suka nuna za su saurari buƙatunmu da suka haɗa da cin zarafi da karɓar kuɗaɗen da jami’an tsaro ke yi na ba gaira ba dalili.
“Saboda haka tunda ba su shirya magance waɗannan matsalolin ba, mun yanke shawarar tsunduma yajin aiki daga safiyar Litinin har sai an yi abun da ya kamata.
https://dimokuradiyya.com.ng/nnpc-ta-mayar-da-farashin-man-fetur-138-62-ga-dilallai/
“Abun takaici ne yadda yajin aikin zai shafi dukkan sauran jihohin Najeriya kasancewar yawancinsu daga nan suke dakon man fetur.
“Ba wai murna muke cewa za mu tsayar da komai ba, amma ba zai yiwu mu ci gaba da zuba ido waɗannan tarin matsalolin na faruwa ba”, cewarsa.
Idan za a iya tunawa, a ranar Juma’a shugaban ƙungiyar NUPENG na ƙasa, Williams Akporeha ya umarci direbobin tankokin man da su dakatar da aiki daga 12 na daren ranar Litinin har sai gwamanti ta saurari kokensu.