Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Liverpool kuma zakarun gasar ajin Firimiyar Ingila ta zazzagawa ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Chelsea ƙwallaye biyu a wasan mako na biyu na gasar ta Firimiya a wannan yammaci na Lahadi.
Wasan dai an tafi hutun rabin lokaci kowacce ƙungiya tana nema, amma bayan an dawo daga hutun rabin lokaci gwarzon ɗan wasan nahiyar Afrika wato Sadio Mane ya jefa Chelsea ƙwallaye biyu a daidai mintina na 50 da kuma 54.
Wannan ƙwallaye guda 2 sune suka tabbatarwa da Liverpool nasararta kuma a yanzu tana da maki 6 da cikin wasanni guda biyu data fafata a kakar wasa ta bana.
An fafata wannan wasa a filin wasa na Stanford Bridge wato filin wasa na ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Chelsea dake birnin London na ƙasar ta Ingila, idan za a iya tunawa a kakar wasan data gabata Liverpool ta wanke Chelsea a wannan filin wasa gashi bana ma ta sake maimaitawa.
A wasan farko dai ana ganin cewar Liverpool ta sha da kyar a hannun ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Leeds United daci 4 da 3 inda ake ganin cewar ba lallai bane ta taɓuka abin kirki a wannan sabuwar kakar wasan ta 2020 zuwa 2021, amma kuma gashi yau ta wanke Chelsea har gida.