
- Ƴan bindiga sun datse kan mai Gadi lokacin da zasu shiga Gidan wani Ɗanmajilisa.
- Ƴan bindigan sun ƙille wuyan mai gadin ne lokacin da zasu shiga Gidan wani Ɗanmajilisa dake Imo.
- Hukumar ƴan sanda ta Imo sun tabbatar da aukuwar lamarin Ekene Nnodimele Ɗan Majalisar jiha dake wakiltar Orsu a jihar Imo tare da tabbatar da ƙillewa mai gadinsa kai.
Shugaban ƴan sandan jahar ya tabbatar ma manema labarai hakan a Owerri a ranar Laraba.
Ɗan sandan yace lamarin ya auku ne misalin ƙarfe ɗaya na dare ranar Laraba.
KUKARANTA:- Ana zargin jami’an Mynamar da bankawa wani ƙauye wuta
Yace suna cigaba da bincike don zaƙulo duk mai hannu a cikin lamarin ya fuskanci hukunci.
Shima Ɗan Majalisar ya tabbatar da hakan lokacin da yake zantawa da manema labarai a garin su dake Orsu.
Yace naji baƙin ciki sosai kan jin labarin kasancewar ƴan ƙauyen ba masu tada zaune tsaye bane.
Ya umarci jami’an tsaron dasu zurfafa bincike sannan su tabbatar da masu hannu acikin aukuwar lamarin.
Sannan ya baiwa mutanen yakin nasa hakuri saboda faruwar lamarin, ya ƙara da cewa da sannu tsaro zai wadata a yakin.
A WANI LABARIN:-
Kamfanin MTN sun ce da akwai samun karancin sabis saboda tashin hankalin dake faruwa a kasar nan kasar nan.
Kamfanin ya bayyana cewar da yiwuwar samun karancin sabis duba da irin rikice-rikicen dake tashi a ko wane yanki dake fadin kasar nan.
Wannan shi zai kawo cikas lokacinda zamu aika masu gyara don cigaban sabis din.
Nigeria tana yin bakin kokarinta wajan fada kungiyar Boko Haram tun bayan sama da shekaru masu yawa, gami da satar mutane don biyan kudin fansa, yin awon gaba da dalibai da kuma tafiya da shanun a yankin kudu maso gabas na kasar najeriya.
A gabas maso arewan dake ƙasar, sannan da jihohin Najeriya ta tsakiya farmakin yan ta’addan ya janyo asarar rayukan mutane wanda ba a san adadinsu ba da miliyoyin kudade