Ƴan Sanda guda biyu da suke aikin bincike a wani wuri akan hanya a ranar Talata da daddare, ƴan bindiga sun buɗe masu wuta a garesu, a yankin Okija a Fatakwal ta Jahar Rivers.
Jami’an guda biyu sun je aiki a wani ofishin ƴan sanda dake Diobu ta Fatakwal.
Lamarin da ya haddasa harin ba za’a iya tabbatar dashi ba, amma wani yace lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 8, yana mai cewa jami’an tsaron sun mutu ne a wurin aikin su.

KARANTA WANNAN LABARIN: Mutane 5 sun mutu Har Lahira, 2 Sun Jikkata, A wani Mummunan Hadari Da Ya Faru A Kano
Wani wanda ya shaida lamarin mai mota ƙirar taxi daya bada sunan shi a matsayin Okey, ya shaida cewa a ranar Laraba da safe, masu kisan sun zone da abun hawa a lokacin da suka ƙaddamar da harin.
Wani mazaunin yankin wanda baison a ambaci sunan shi sabudda halin tsaro, yace ƴan bindiga sun je ta hanyar D/Lime a Fatakwal.
Yace bayan mintoci 15 da faruwar lamarin, tawagar ƴan sanda sun iso wurin da motar fatrol, wanda yasa ya ruga sabudda tsoron kada a kama shi.
A lokacin da aka tuntuɓe shi, Mai Magana da Yawun Rundunar Ƴan Sandan Jahar Nnamdi Omoni ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ƙara dacewa jami’an tsaron suna gudanar da aikin ne a lokacin faruwar lamarin.