Wasu ƴan bindiga sun kashe a ƙalla ƴan sanda guda 7 a wani Kwantan ɓauna da suka yi, kusa da ƙauyen Zonai dake gundumar Magami ta Ƙaramar Hukumar Gusau dake Jahar Zamfara.
Ƴan sandan kamar yadda mazauna yankin suka shaida, sun dawo ne daga wajen aiki a wani wuri da suka kafa sansanin su a ranar Litinin, kusa da ƙauyen Zonai akan hanyar Gusau-Magami-Ɗan sadau, a lokacin da ƴan bindigar suka buɗe masu wuta a ababen hawan su dake ɗauke da jami’an.
“Abin baƙin ciki ne musamman gare mu a garin Magami, saboda ƴan sanda sun taimaka matuƙa gaya wajen kawo ɗauki a lokacin mummunan matsalar tsaro a yankunan.

KARANTA WANNAN LABARIN: Ƙarancin Man Fetur yana cigaba da ƙamari a Yobe, a yayinda farashin Litar mai ya ƙaru
“A taƙaice kasancewar su a wurin da suka yada sansani, ya ƙara ƙwarin gwuiwa ga matafiya subi hanyar. An kashe matafiya da dama, wasu kuma anyi garkuwa dasu akan hanyar mai tsawon kilomita 50 daga Gusau zuwa Magami. Dagaske abun baƙin ciki ne,”inji wani mazauni da ake kira Halliru.
Mai magana da yawun Rundunar Ƴan Sandan Jahar SP Muhammad Shehu ba’a same shi ba, domin jin ta bakinsa ya zuwa lokacin haɗa wannan rahoton.
Haka zalika, Mai Magana da Yawun Asibitin Yariman Bakura Awwal Usman Ruwandoruwa ya shaidawa Majiyar Jaridar Dimokuraɗiyya cewa, an kawo gawarwakin ƴan sandan da suka rasu da misalin ƙarfe 8 na ranar Talata.