Wasu ƴan ta’adda da ake kyautata tunanin Fulani ne, sun sace matafiya da har yanzu ba’a san ko nawa ne, akan hanyar Sapele-Warri ta Jahar Delta.
Wanda ya shaida lamarin, yace ya faru a ranar Asabar. Amma Rundunar Ƴan Sandan Jahar Delta ta musanta sanin sace matafiyan a Jahar.
Wani daga cikin wanda ya tsallake rijiya da baya daga hannun masu garkuwa da mutanen, amma ya samu raunuka a lokacin lamarin, ya bayyana cewa Fulanin sun kai wa matafiyan hari a lokacin da suka taho da yawansu.

KARANTA WANNAN LABARIN: Sunayen Wayoyin da Za su Dena Yin WhatsApp Nan da Awanni Kadan
Wani da lamarin ta faru dashi, a lokacin da yake magana a cikin wani bidiyo a kafar sadarwa ta Facebook, yace masu kai harin sun harbe shi da bindiga, tare da tafiya da iyalan sa.
Ya ƙara dacewa, wanda suke cikin motar suma an sace su gaba ɗaya.
A lokacin da aka tuntuɓe shi, Jami’in Hulɗa da Jama’a na Rundunar Ƴan sandan Jahar Delta DSP Bright ya musanta sanin gudanar da wannan lamari a jahar.
Yace “babu wani rahoto akan lamarin”
Comments 1