Wata Babbar Dabar Ƴan bindiga da ake kira da Angry Vipers, sun yi gargaɗin hari ga Fitaccen Ɗan Kasuwar nan ɗan asalin Jahar Anambra Obi Cubana sakamakon ganin sa da akayi da Mataimakin Kwamishinan Ƴan sanda Abba Kyari a wajen binne gawar Mahaifiyar shi
Binne gawar wadda ta gudana a Oba, Jahar Anambra a watan juli na Shekarar 2021, an nuna dukiya a yayinda Obi Cubana ya binne gawar Mahaifiyar sa a wani.

KARANTA WANNAN LABARIN: Mutane Uku Sun Mutu A Hatsarin Mota A Hanyar Ilorin Zuwa Jebba
An ga da dama daga cikin fitattun Ƴan wasan Kwaikwayo da Mawaƙa da dama, da ƴan kasuwa, da ƴan siyasa, sun fito domin rufe gawar, ciki har da Abba Kyari, a yayinda hoton Obi Cubana aka ganshi a tare.
Daya ke maida martani akan ganin Kyari a bikin binne gawar, Ƙungiyar Ƴan ta’addan yayi nuni dacewar Obi Cubana nan bada jimawa ba zaiji daga gare su.
A cikin wani bidiyo daya fita a kafar sadarwa ta zamani, Angry Vipers tace ” zuwa ga Sarakai da manya a ƙasar mu, Waɗanda suke aiki da masu kashe mana matasa, kai da mutanen ka, sun tabbatar dacewa Abba Kyari ya dawo Jahar Anambra, zakaji daga garemu.