Dattijo a Jihar Katsina Alhaji Abu Ɗanmalam Karofi bayyana cewa wasu masu hana ruwa gudu ne ke hana shirye-shiryenda Gwamnatin Shugaba Buhari ta ɓullo da su na yaki da fatara, su isa ga talakawa.
Alhaji Abu Ɗanmalam Karofi na magana ne a sa’ilinda yake zantawa da wakilin Jaridar Dimokuraɗiyya a gidansa dake Katsina.
Kamar yadda Karofi ya bayyana, tunda aka ƙirƙiri tarayyar Najeriya ba’a taɓa shugaba da ya ɓullo da dumbin shirye-shiryen inganta rayuwar al’umma ba kamar Shugaba Muhammadu Buhari.

KARANTA WANNAN LABARIN: Tsohon Ministan Noman Najeriya Abba Sayyadi Ruma ya rasu
Sai dai a cewarsa masu zagon ƙasa da son zuciya suna amfani da damar su na ganin shirye-shiyen basu iso akan talakawa wanda akayi domin su.
Ya nuna damuwa akan wasu masu riƙe da muƙamai da irin waɗannan shirye-shirye suke a ƙarƙashin ofisoshinsu, da suke ko in kula da danne wasu batutuwa, wanda hakan ya taimaka wurin ƙaruwar talauci a ƙasar nan.
Alhaji Abu Danmalam Karofi ya buƙaci ƴan Najeriya akan su kasance masu addu’a akan Allah ya ƙara jagoranci ga shugaba Buhari, su kuma masu hana ruwa gudu Allah ya shiryesu.
Akan matsalolin tsaro a Katsina, Alhaji Abu Danmalam Karofi ya yabawa Gwamna Masari akan tsauraran matakai da ya dauka na shawo kan matsalolin da ke addabar jihar akan tsaro.
Ya nuna damuwa akan halayyar wasu mutane na taimakawa ƴan ta’adda da kayan amfanin yau da kullum, sai ya horesu akan suji tsoron Allah su daina aikata hakan.
Alhaji Abu Danmalam Karofi yayi addu’a akan Allah SWT yayi jagoranci ga Gwamna da kuma jami’an tsaro wajen ganin an shawo kan matsalar.