Ƴan Najeriya Masu zama waje sun fi kowa Hankali, Ilimi a Amurka, Burtaniya – NiDCOM
Hukumar kula da Ƴan ƙasa mazauna Ƙasashen Waje, NiDCOM, ta bayyana cewa ƴan Nijeriya mazauna ƙasashen ƙetare a matsayin waɗanda su ka fi kowa hankali da ilimi a Amurka da Birtaniya.
KARANTA WANNAN LABARIN: INEC tace Jahar Kano itace tafi kowacce jiha yawan karɓar Katin Zaɓe
Shugabar hukumar, Abike Dabiri ce ta bayyana hakan ne a yau Laraba a Abuja, a wani taron manema labarai domin sanar da Bikin Ranar Mazauna Ƙasashen Waje na 2022.
An shirya gudanar da bikin ne a ranar 25 ga watan Yuli.
Taken bikin shi ne: “Hoɓɓasar Al’umma a Zamani a kan Kalubalen Ci gaban Ƙasa”.
Ta ce ƙwararru na ci gaba da masu kishin kasashen waje a fadin duniya sun yi nuni da cewa babu wata kasa a duniya da za ta ci gaba ba tare da taimakon al’ummarta mazauna ƙasashen waje ba.
A cewarta, ’yan kasashen waje sun kasance masu albarka ga kasarsu.
Don haka, ta ce, ƴan Najeriya mazauna kasashen waje su na ba da gudummawa sosai ga haɓɓakar tattalin arzikin ƙasar.