Ƴan sanda a Abuja sun kama wani ɗan daba daya ɓalle mota domin ya saci wasu kayayyaki masu mahimmanci.
Haka zalika, Rundunar Ƴan Sandan Babban birnin Tarayya Abuja ta gano na’ura mai ƙwaƙwalwa ƙirar Laptop guda 75, da sauran wasu kayayyaki ga wasu da ake zargi.
Dayake jawabi akan kama mutanen a Abuja a ranar Talata, Kwamishinan Ƴan sandan Babban birnin Tarayya Sunday Babaji, yayi nuni dacewa, an ƙwato motoci 6 da wata tawagar ƴan ta’adda ta sace a wurin ajiye motoci da makulli mai buɗe kowacce mota wato ‘master key’.

KARANTA WANNAN LABARIN: DA Dumi-duminsa: Bam Ya Sake Tashi A Gidan Yarin Jihar Oyo
Dayake bada bayani akan yadda aka samu nasarar, Kwamishinan Ƴan sandan yace a ranar 12 ga watan Oktoba na shekarar 2021, ƴan sanda sun kama wani Abubakar Shettima mai shekaru 28, inda ya tabbatar cewa ya ƙware wajen buɗe motocin mutane, tare da kwashe masu kayayyakin su, musamman da suka haɗa da Laptop da wayoyi ƙirar Tablets da jikkuna.
“Bincike ya nuna cewa Abubakar nada waɗanda suke sayen kayayyakin sa, inda acewar sa yana sayar da kayayyakin ga wani Adekoye Anthony ɗan shekaru 28 da Yusuf Isa ɗan shekaru 26, wanda su kuma suna sayar da kayayyakin da ɓalli-ɓalli.
Dukkanin waɗanda ake zargin sun tabbatar da laifin da ake zargin su da aikatawa, za’a kuma kaisu kotu bayan an gudanar da bincike.
Ƴan sanda sunce sun sami wata bindiga ƙirar Fistin ga wani Saliu James, wanda ake zargin yana yin ƙwacen mota a marabar Nyanya ba Babban birnin tarayya Abuja.