Hukumomin Ƴan sanda sun gurfanar da wani lauya mai shekaru 49, Etomike Ndigwe, a gaban wata kotun Majistare ta Otuocha da ke Jihar Anambra, bisa zarginsa da takardun bogi.
Ana tuhumar Ndigwe da tuhume-tuhume guda uku da suka haɗa da jabu, haɗa baki da kuma keta zaman lafiya, laifukan da za a hukunta shi a ƙarƙashin sashe na 443 da 115 na kundin laifuffuka na Cap 36 Vol. II Dokar Jihar Anambara 1991.
Ɗan Sanda mai shigar da ƙara,Richard Okoti, ya shaida wa Kotun cewa wanda ake zargin ya aikata laifin ne a ranar 29 ga watan Yuni a Aguleri, na Ƙaramar Hukumar Anambra ta Gabas.
KARANTA WANNAN LABARIN: Amurka ta tabbatar da hallaka shugaban AlQa’ida, yayin wani luguden wuta a Afghanistan
Okoti ya ce wanda ake tuhumar ya yi jabun takardar shaidar rajistar unguwa, kuma ana zarginsa da yin amfani da makamancin haka domin ya nuna shi ɗan unguwar Aguleri, karamar hukumar Anambra ta Gabas.
Ya kuma yi zargin cewa wadanda ake zargin yana nuna kansa ga jama’a a haka domin haifar da rashin zaman lafiya a tsakanin jama’a ta hanyar cire sunan sa mai ɗauke da titin Dr Innocent Chidumebi Okonkwo, wanda aka dora a kan gidaje a kan titi.
A cewarsa, babu wata takardar shaidar da aka ce shi ɗan Ƙaramar Hukumar.
Lokacin da aka karanta wa wanda ake tuhumar ya ƙi amsa laifin da ake tuhumarsa da shi, kuma Alkalin kotun, Mista M.I. Ogolo ya bayar da belinsa tare da waɗanda suka tsaya masa.
An ɗage sauraron ƙarar zuwa ranar 5 ga watan Agusta domin cigaba da shari’a.