Jami’an ‘yan sandan da ke aiki da rundunar ‘Operation Restore Peace’ sun tarwatsa wani sansanin masu garkuwa da mutane a dajin Galadimawa da ke karamar hukumar Giwa a jihar Kaduna.
A cewar ‘yan sandan, wani kazamin arangama da aka yi ya kai ga kama wani da ake zargin dan fashi da makami tare da kwato bindigogi biyu masu dauke da albarusai, kamar yadda jaridar Daily trust ta rawaito.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, DSP Mohammed Jalige, ya tabbatar da faruwar lamarin a wata sanarwa da ya fitar a ranar Asabar din nan, inda ya ce an kai harin ne a ranar 18 ga watan Agusta.
Ya ce wasu daga cikin ‘yan fashin sun tsere zuwa cikin dajin da raunuka daban-daban.
‘Yan Bindiga Sun Tilastawa Mazauna kauyuka 8 Barin Mahallansu
“Jajirtattun jami’an sun yi nasarar cafke daya daga cikin ‘yan fashin mai suna Yusuf Monore namiji dan shekara 20 dauke da bindigu kirar AK 47 da 49 guda 2, da harsashi guda biyar 7.62 X 39mm. Sauran abubuwan da aka kwato sun hada da wayoyin hannu na Techno guda uku da fitilar wuta,” inji shi.
Dimokuradiyya ta rawaito cewa, Jalige ya ce ana ci gaba da gudanar da cikakken bincike a kan wanda ake zargin yayin da jami’an tsaro suka bi bayan ‘yan bindigar da suka gudu.
Ya ce kwamishinan ‘yan sanda, CP Yekini Ayoku, a lokacin da yake yaba wa irin rawar da jami’an da suka gudanar da aikin, ya bukaci a samar da hadin kai a tsakanin jami’an tsaro a jihar.
Hakazalika kwamishinan ya kuma umarci ’yan kasa masu bin doka da oda da mazauna jihar da su kasance a koyaushe kuma su yi taka-tsan-tsan tare da kai rahoto ga hukumomin tsaro cikin gaggawa.