Ƴan sandan jihar Kebbi sun ƙaryata zargin da ake yi kan cewa ƴan bindiga sunyi amfani da motar su wajan kwashe Ɗalibai da Malamai.
Ƴan sandar jihar Kebbi sun ƙaryata zancen dake yawo kan cewar ƴan bindiga sun yi amfani da motar ƴan sanda a lokacin da suka sace Ɗaliban 50 na Makarantar Yawuri dake Kebbi.
A cewar Nafi’u Abubakar ɗan sandan yace motar da ƴan bindiga sukai amfani da ita sun ƙwace tane wajan wani babban Alƙali dake Kebbi tare da rubutun “Kebbi State Judiciary” Mai lamba KBSJ 29.
Ya ƙara da cewa hukumar ƴan sandan zasu cigaba da bayyana lamarin akai akai.
Ya cigaba da cewa ƴan sandan zasu ƙulan ƙawance da sauran takwarorinsu don tabbatar da kuɓutar waɗanda aka sace.
A wani labarin:- Anyankema wata mata Hukuncin watanni shida a gidan kaso bayan banakwa gidan Amaryar tsohon mijinta wuta
Matarmai suna Zainab ibrahim an yanke mata hukuncinne a wata kotun Shari’ar Musulunci dake Rigasa a Kaduna
ZainabIbrahim ta kona gidan Amaryar tsohon Mijinta tare da wasu kayayyakin amfaninta
Alkalin kotun Abubakar-Tureta ya bukaci Zainab da ta biya diyyan kayan data kona nai naira Dubu Dari da Talatin da Daya
Wata Kotun Shari’ar Musulunci da ke zaune a Rigasa, Kaduna a ranar Laraba ta yanke wa wata mata ’yar shekara 34,mai suna Zainab Ibrahim, hukuncin daurin watanni shida saboda kona gidan tsohuwar matar tsohon mijinta, rahoton DN.
Alkalin kotun, Salisu Abubakar-Tureta ya yanke wa Zainab hukuncin ne bayan ta amsa laifukan da suka shafi ke ta haddi da barna ta hanyar wuta.
Alkalin ya bai wa mai laifin zabin tarar N10,000.
Mista Abubakar-Tureta ya kuma umarce ta da ta biya N131,000 a matsayin diyyar kone wasu kayayyakin amfani Mallakar Maryam Ramalan.
An yanke uwargida hukuncin daurin watanni 6 bayan kona gidan Amaryar tsohon mijinta
Tun farkon lamarin, lauya mai shigar da kara, Insp Sambo Maigari ya fada wa kotun cewa laifin ya saba wa Sashi na 174 da 373 na Laifi.
Ya ce mai laifin ta amsa cewa ta yi amfani da fetur ne wajen kona gidan sabuwar amaryar saboda Zafin kishi, riwayar Pulse.
A cikin rokon ta na neman yafiya, ta yi iƙirarin cewa ta kasance mace mai biyayya ga tsohon Mijinta,