Gwamnan Jahar Zamfara Bello Matawalle yace ƴan siyasa ne ke haddasa tsaiko ga shirin sasanci daya yi da ƴan bindiga a Jahar.
Matawalle ya bayyana haka a wani shirin tattaunawa na gaggawa da gidan rediyo na Radio Now 95.3 ya gabatar a ranar Juma’a.
Gwamnan yace ƴan siyasa da suke da haɗin kai da ƴan bindiga, sun gaya masu kada su yarda da abinda Gwamnati ke cewa.

KARANTA WANNAN LABARIN: Mathematics zai iya magance Matsalolin tsaron Najeriya — Cewar wani Masanin Lissafi
Yace “bayan mun ɓullo da shirin sasanci, ya kamata ya zama kowa na bada gudunmawa a tsakanin gwamnati, al’ummar jahar, da ƴan siyasa, amma abun baƙin ciki, a lokacin da gwamnati ke bakin ƙoƙarin ta na ganin an samu zaman lafiya, wasu ƴan siyasa na tunanin basa so mu samu nasara.
“Suna yin munanan kalamai akan sasancin, kuma wasu daga cikin su, suna haɗin baki da ƴan ta’addan, kuma sun gaya masu abubuwa na kada su amince da shirin sasanci na Gwamnati.
Matawalle wanda yana ɗaya daga cikin waɗanda suka yi kiran sasanci da ƴan bindiga dake addabar yankin Arewa Maso Yamma na Najeriya, ya taɓa shaidawa kamfanin Dillancin Labaru na Ƙasa a watan Ogusta cewa shirin sasancin ya haifar da ɗa mai ido a Jahar.
Ya kuma canja matsayar sa a watan Satumba a lokacin da ya sanar da cewa Gwamnatin sa bazata yi afuwa da ƴan bindiga, tunda sunƙi amfani da ƙaramcin da akayi masu.
Gwamnan ya kuma bayyana cewa jami’an tsaro sun samu tabbaci daga “masu bada bayanan sirri guda 2000” wanda suka bayyana cewa akwai ƴan siyasa