Yan bindiga daɗi da ake kyautata zaton Fulani ne, sun kai hari a ƙauyukan Madamai da Abun, dake ƙaramar hukumar Ƙaura ta jahar Kaduna, tare da kashe aƙalla Mutane 30.
Sun kai harin ne a ranar Lahadi da yamma, inda suka afkama ƙauyuka guda biyu.
Mata da ƙananan yara sune waɗanda akafi kashewa a lokacin da yan bindigar suka buɗe wuta, kamar yadda majiyar jaridar Dimokuraɗiyyar ta ruwaito.
KARANTA WANNAN LABARIN: NDLEA ta gurfanar da Mai shekara 28 a gaban Kotu, bisa safafar Tabar Wiwi
Babban Fada na cocin katolika ta Diocese Micheal Magaji dake kafanchan ya bayyana cewa, yan bindigar sun zo ne a ƙauyen da yawa.
Ya tabbatar dacewa, sun ƙone gidaje da dama, kuma ba za’a iya tabbatar da ko nawane suka ƙone.
Ya kuma ce bazai iya tabbatar da ko mutane nawa lamarin ya rutsa dasu ba, amma yace an ɗauki waɗanda suka ji raunuka zuwa Asibiti domin karbar magani.
Sanata mai wakiltar Kaduna ta kudu Ɗanjuma La’ah ya yi Allah wadai da babbar murya, na cigaba da kisa gami da ƙone dukiyoyin al’umma a kudancin Kaduna.
Ya bayyana damuwa cewa mutanen kudancin Kaduna sun daɗe suna fama da yawaitar harin ƴan ta’adda a lokuttan da suka wuce, inda suka kashe ɗaruruwan mutane, tare da korar mutane daga garuruwan su.
Sanatan yayi kira ga mutanen yankin dasu kasance masu haƙuri, kuma kada su ɗauki doka a hannun su.
Ya buƙaci hukumomin da lamarin ya shafa, dasu tabbatar da tsaro a yankin domin magance cigaba da kai harin, wanda ya janyo rasa rayuka da dukiyoyin al’ummar yankin.
Yace idan gwamnati ta kasa ɗaukar mataki, to mutane basu da wani zabi illa su kare kawunan su.