Ƴan Ta’adda sun kori wani Sansani mai Sojoji 80 a Borno, sun gudu da Makaman su
Ƴan ta’adda da ake kyautata zaton Ƴan ISWAP ne a ranar Laraba sun kori wani sansanin Soji a Jahar Borno.
Daily Trust ta gano cewa Ƴan ta’addan sun kai wa Sojojin hari a ƙauyen Ajiri ta Ƙaramar Hukumar Mafa da misalin ƙarfe 9 na dare, inda suka sanya da tsiya sojojin suka ruga da raunuka da dama.
KARANTA WANNAN LABARIN: Ƴan Daba sun Jikkata Mutane 3 wurin Karɓar Katin Zaɓe a Osun
Majiya tace kimanin sojoji 80 suka ruga Suka bar Sansanin su, tare da barin manyan makaman su da wasu kayayyaki nasu da suka haɗa da wayoyi, wanda dukkanin su ƴan Ta’addan sun kwashe su.
Sojojin sun kasa tsayawa domin tunkarar sojojin, sakamakon rashin Harsashi da kayayyakin yaƙi.
“Ƴan ta’adda sun fi ƙarfin Dakarun Soji, wanda suka ruga suka bar harsashi da makamai.
Mazauna yankin sun ce ƴan ta’addan wanda suka karɓe iko da ƙauyen Ajire da misalin ƙarfe 9 na dare zuwa ƙarfe 4 na safiya a ranar Alhamis,amma basu harbi farar hula ba, sai dai sun kwashe kayayyakin su.
Comments 1