Ƴan Ta’adda sun tare hanyar Kaduna, sun kashe mutum 2, sun sace wasu
Wasu Ƴan ta’adda sun tare hanyar Birnin-Gwari zuwa Funtua a karamar hukumar Birnin-Gwari a jihar Kaduna, inda suka kashe mutane biyu tare da yin awon gaba da wasu da dama.
KARANTA WANNAN LABARIN: B/Haram Sun Shiga wani hali suna fama da Ƙarancin Abinci, Makamai, bayan Ambaliyar Ruwa
Shugaban kungiyar masu ci gaban masarautar Birnin-Gwari (BEPU), Ishaq Kasai, a wata sanarwa da ya fitar a ranar Litinin, ya ce ‘yan ta’addan sun kashe wani Direba tare da sace matafiya da dama.
Ya ce ‘yan bindigar sun tare hanyar ne tun ranar Alhamis da ta yi daidai da ranar kasuwar Birnin-Gwari, inda suka kashe wani direba tare da yin garkuwa da matafiya da dama.
“Har yanzu hanyar ba ta da hanyar wucewa. Kamar yadda yake a yanzu, galibin al’ummomin da ke kan wannan titin kamar Kwasa-kwasa, Marabar Kwasa-kwasa, Nacibi, da Farin Ruwa da dai sauransu, suna fama da fargabar ko wani abu zai faru,” in ji Kasai.
Ya kuma bayyana cewa ‘yan bindigar sun kai hari a garin Damari a ranar Asabar da misalin karfe 10 na dare, inda suka kashe mutum daya tare da kwashe kayayyakin shaguna da dama.
Don haka Kasai ya ce akwai bukatar tura sojoji zuwa yammacin Birnin-Gwari, musamman a yankin Kakangi da Randagi da ke da iyaka da jihohin Zamfara da Neja.
A yayin da yake yaba da sabon kokarin gwamnati da dakarun sojojin, shugaban kungiyar ta BEPU, ya bukaci a tsawaita aikin zuwa maboyar ‘yan ta’addan a cikin dazuzzukan domin dawo da zaman lafiya domin jama’a su zauna a cikin al’ummarsu ba tare da tsoro da fargaba ba.
A wani labarin kuma: An Buƙaci APC ta sake duba Tikitin Takarar Shugaban Ƙasa
Gamayyar masu ruwa da tsaki a shiyyar Arewa maso Gabas da Arewa ta Tsakiya na jam’iyyar APC, sun buƙaci kwamitin ayyuka na jam’iyyar APC (NWC), da ya gaggauta sake duba zaben Sanata Kashim Shettima a matsayin dan takarar mataimakin shugaban kasa na jam’iyyar.
Babban sakataren kungiyar Dauda Yakubu, yayin da yake zantawa da manema labarai a Abuja ranar Litinin, ya shawarci jam’iyyar da ta gaggauta yin wani abu don magance matsalar da ta kunno kai sakamakon matakin da ta dauka a kan tikitin takarar shugaban kasa na Musulmi da Musulmi.