Wata tawaga daga Daura, garin Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari dake Jahar Katsina, sun yabawa Gwamnan Jahar Kogi Yahaya Bello da irin cikakkiyar soyayyar sa ga Shugaban Ƙasa.
Tawagar data ƙunshi Dattawa da masu ruwa da tsaki a ɓangaren siyasa daga Daura, sun kai ziyarar ne ga Gwamna Yahaya Bello a ranar Alhamis.
Da suke jawabi ta bakin Mai Magana da Yawun su, Injiniya Mato Daura yayi nuni dacewar Soyayyar Gwamna Yahaya Bello ga Shugaban Ƙasa Muhammadu aba ce data daɗe, ta dalilin dangantakar shi ta kusa, irin wannan soyayya, da kyawawan halayen sa, ana koyen su.

KARANTA WANNAN LABARIN: ‘Yan bindiga sun kashe Mutane uku, sun kona kekuna a yankin Imo
Mato yayi kira ga Gwamna Bello daya futo Takarar Shugaban Ƙasa a Babban Zaɓen Shekarar 2023, suna masu bashi tabbacin cewa, ƙungiyar zata yi iya bakin ƙoƙarin ta na goyon bayan shi a matsayin ɗan takarar daya fi kowane cancanta.

A jawabinshi, Gwamnan ya godema tawagar da irin wannan ziyarar yabawa ga soyayyar shi da Shugaban Ƙasa, yana mai ƙara dacewa marar godiya ne kaɗai ne bazai yabawa aikin Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ba.