By Ishaq Dabai
Kimanin mutane uku masu kwacen mota aka kama wadanda ake zargi da kashe wani UBER direba dan shekara 27 mai suna Mirenikeji Stephen Oluwaniyi a jihar Legas.
Wadanda ake zargi da aka bayyana sunan su Taiwo mai shekaru 23 da kuma Rilwan Nasir mai shekaru 27 ana zargin su da kashe mai motar kirar Toyota Corolla Saloon.
Tuni dai jami’an ‘yan sanda suka kama wadanda ake zargin inda aka tsaresu a ofishin ‘yan Sanda na Meiran dake jihar Legas.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan Sanda na jihar Legas Adekunle Ajisebutu ya tabbatar da faruwar lamarin inda yace an kama masu laifin da suka kashe direban UBER kuma an kaisu Meiran dan su girbi abinda suka shuka.
Ya kara da cewa wadanda ake zargi sun dauki gawar wanda suka kashe inda suka jefashi a gadar Abule Egba kusa da jihar Legas dake kan babban titin Abeokuta.