Wani bidiyo da aka sanya a Instagram ya nuna wata yarinya ƙarama wacce Allah ya yiwa wata irin baiwa ta musamman.
Yarinyar mai suna Mimi, Allah yayi mata baiwar ƙorayen idanuwa, waɗanda suka ɗauki hankulan mutane sosai. Rahoton jaridar Legit.ng
KU KARANTA KUMA: CBN Ya Yi Amai Ya Lashe, Ya ce Bankuna Su Karbi Tsofaffin N500, N1000
Wata mai kula da yara masa galihu sosai, mai suna Tusaiwe Yana, itace ta sanya bidiyon Mimi a Instagram.
A cikin bidiyon yarinyar tayi ƙoƙarin rerawa Tusaiwe wata waƙa amma ta manta baitukan waƙar.
Lokacin da Tusaiwe ta tuna mata sunan waƙar, sai ta fara rerata cikin wata murya mai daɗi.
Wani abu da yarinyar da take da shi ma musamman shine korayen idanuwanta masu ƙyalli.
Mutanen da suka kalli bidiyon sun bayyana cewa sun fi mayar da hankali kan korayen idanuwanta a maimakon waƙar da take rerawa.
Wasu daga cikin su sun ce idanuwanta sun yi kama da wata wacce ta fito a cikin shirin fim ɗin nan mai suna Avatar.
Ba a tabbatar da cewa idanuwanta haka aka haifeta da su ba,a amma an bata kyautar tubarau a cikin bidiyon.
CBN Ku Taimaka Min Fasinjoji Sun Lafke Ni Da Tsofaffin Kuɗi -Direba Ya Koka
A wani labarin na daban kuma, wani direban motar haya ya nemi ɗaukin gaggawa bayan da fasinjoji suka lafke shi da tsofaffin kuɗi.
Wani matashi ɗan Najeriya mai tuƙin motar haya a jihar Legas, ya koka kan ƙarancin sababbin kuɗi da kuma tsofaffin takardun N1000 da N5000 da aka ɓatar da su.
A cikin wani bidiyo da ya sanya, matashin ya ce fasinjojin sa sun kasa samun sababbin kuɗin, kuma har yanzu tsofaffin kuɗi suke bashi waɗanda aka daina amfani da su.