A yayinda Nigeria ke fama da matsin tattalin arziki, Ministan Noma da cigaban Karkara Dr Mohammed Abubakar a ranar Juma’a ya bayyana cewar, an cire ƴan Nigeria fiye da miliyan 2 daga ƙangin talauci ta hanyar ɓangaren noma a cikin shekaru biyu da suka gabata.
Abubakar ya bayyana haka a lokacin da yake jawabi ga Manema labaru, domin bikin ranar abinci ta duniya ta Shekarar 2021 da taken “aikin mu na yanzu shine na nan gaba, samar da ingantaccen abinci, muhalli da kyakkyawar rayuwa.
Ya bayyana cewar an ɓullo da wani tsari na inganta harkokin noma na zamani wato- NATIP, da zai karaɗe shekara ta 2021 zuwa 2025 domin inganta amfani da ake samar wa tsakanin hukumomin dake bincike da manoma.
KARANTA WANNAN LABARIN: Satar Kaddarorin Coci: Kotu ta daure wani na tsawon watanni 6 a Legas
Yace “ɓangaren noma shine kaɗai ɓangaren daya samu bunƙasa a lokacin dokar kulle ta Covid-19 da gudunmuwa 24.23 na tattalin arzikin ƙasar.
Ƙari bisa ga haka ta hanyar shirye-shirye da dama na harkokin noma, mun fitar da ƴan Nigeria miliyan 4,205, 576 daga ƙangin talauci a cikin shekaru biyu, kuma wannan zai cigaba, a matsayin wani ƙoƙari na shugaban ƙasa Muhammadu Buhari na fitar da ƴan Nigeria Miliyan ɗari 100 daga ƙangin talauci a cikin shekaru 10 masu zuwa.