Daga: Abbas Yakubu Yaura
Tsohon Firaministan Japan, Shinzo Abe, wanda aka harbe shi a lokacin da yake jawabi gabanin zaben majalisar dattawa da za a yi ranar Lahadi, ya mutu.
An harbe Abe a kirji da kuma wuyan sa ranar Juma’a a yammacin Japan.
Ya fadi ne a kan titi, inda jami’an tsaro da dama suka ruga zuwa gare shi, a cewar jaridar Guardian UK.
KARANTA WANNAN LABARIN: https://dimokuradiyya.com.ng/yanzu-yanzu-gwamnatin-tarayya-ta-fitar-da-sunaye-da-hotunan-%c6%b4an-taaddan-da-suka-tsere-daga-yarin-kuje/
Kafar yada labaran ta nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na NHK cewa, wani babban jami’in jam’iyyar Liberal Democratic Party, ya rasu ne a asibitin da yake jinya.
Rahotanni sun bayyana cewa harin an kai shi ne a birnin Nara.
Hotunan bidiyo sun nuna jami’an tsaro da ke wurin suna tunkarar dan bindigar wanda yanzu haka yake hannun ‘yan sanda.
Harin da aka kai kan Abe, wanda shi ne firaminista mafi dadewa a kasar Japan, ya girgiza kasar.
Tun da farko, Firaminista Fumio Kishida ya yi Allah wadai da matakin a wani taron manema labarai, ya kara da cewa, “Abe na cikin mawuyacin hali. Ina addu’ar ya tsira.”
A Wani Labarin Kuma Kwamitin Uba Sani a Majalisar Dattijai ya tantance Umar Yahaya a matsayin Shugaban Hukumar UFTF
Sanata Uba Sani mai Wakiltar Kaduna ta tsakiya a Majalisar Dattijan Najeriya kuma Ɗan Takarar Gwamnan Jihar Kaduna ƙarƙashin Jam’iyar APC ya cigaba da aikin sa na kwamitin Majalisar Dattijai gadan-gadan, a ƙoƙarin sa na sauke nauyin dake rataye a wuyan sa.
A ranar laraba ne dai Sanatan tare da membobin Kwamitin, suka tantance Umar Yahaya a matsayin Shugaban Hukumar UFTF.
Sanatan ne ya bayyana haka a Shafin sa na Twitter.
“A yau ne Kwamitin Majalisar Dattawa mai kula da harkokin banki, inshora da sauran cibiyoyin kudi da shugabanta ya yi nasarar tantance, wanda Shugaban Ƙasa ya aiko Mana Umar Yahaya, domin tabbatar da shi a matsayin mataimakin shugaban hukumar kula da asusun bai-daya (UFTF)”.
Uba Sani yace “An yi ma wanda aka naɗa tambayoyi da dama kan kalubalen da tattalin arzikin Najeriya ke fuskanta da kuma gudunmawar da Hukumar Kula da Asusun Tallafin Kudin (UFTF) za ta iya bayarwa wajen kokarin farfado da tattalin arzikinm”.
“Wanda za’a nadan ya nuna matukar fahimta kan muhimman batutuwa, Sharhinsa yayi dai-dai kuma Ba a sami koke ko suka game da wanda Shugaba Buhari ya turo.
Sanata Uba Sani ya miƙa godiya ta musamman ga Majalisar Dattawan Najeriya. Yace “Kwamitin na son miƙa godiyar sa ga majalisar dattawa bisa wannan damar da ta bamu na yin wannan aiki.