Ɗan shekaru 25 Prince Mohammed Kadade Suleiman ya zama Shugaban Matasa na Jam’iyyar PDP na Ƙasa.
Suleiman wanda ya kasance ɗan Asalin Jahar Kaduna, Shiyyar Arewa maso Yamma ta Nigeria, ya zama shugaban matasa bayan an yi sasanci a Zaɓen Shuwagabannin Jam’iyyar na Ƙasa da aka gudanar a ranar Asabar a Abuja.
Zaɓen wanda aka kammala a ranar Asabar da safe, ya samu tsohon shugaban Majalisar Dattijai Iyorchia Ayu a matsayin shugaban jam’iyar na ƙasa.

KARANTA WANNAN LABARIN: Iyorchia Ayu ya zama Shugaban Jam’iyyar PDP na Ƙasa
A yayinda Umar Damagum ya zama Mataimakin shugaban Jam’iyyar na yankin Arewa, sai Taofeek Arapaja ya zama Mataimakin Jam’iyyar na Kudu.