Jarumi Akshey Kumar ya kasance mai yin fim kuma mai yin barkwanci a fina-finai sannan kuma ya kanyi fim ɗin soyayya da sauransu, jarumi ne da aka haife shi a ranar 9 ga watan Satumba na shekarar 1967 inda sunansa na gaskiya shine Rajib Hari Ombatia sannan kuma ana yimasa laƙabi da Akki ko Raju kokuma Khiladi Kumar.
Ayanzu haka yana da ‘ya’ya guda biyu da namiji mai suna Aarav wanda aka haife shi a shekarar 2002 inda yanzu yana da shekaru 18 sai kuma ‘yar sa mace mai suna Nitara wadda aka haife ta a shekarar 2007 inda yanzu tana da shekaru 13 kenan inda matar Akshey Kumar ce ta haifar masa su wato Twinkle Kanna.
Shidai wannan ɗa na Akshey Kumar ya bayyana cewar bayason a dinga haska shi a kafar yaɗa labarai kamar yadda ake haska mahaifinsa, sannan kuma ya ƙara da cewar bayason yayi dogaro da kayan mahaifinsa kokuma ya dinga taƙama da tinƙaho kan cewar babansa shahararre ne duniya ta sanshi.
Aarav ya ce “kamar yadda kowa ya sani a wannan duniyar ta yanzu zakaga ‘ya’ya suna tinƙaho da kuɗin mahaifinsu ko sunansa to ni babu ruwana da wannan kawai nafi son naje na nemi nawa da kaina kokuma nima nayi suna kamar yadda mahaifina yayi amma babu ruwana da jingina dashi nafi son nima na kafa kaina kamar yadda shima mahaifin nawa ya kafa kansa”
Shima mahainfin Aarav wato Akshey Kumar ya bayyana cewar ɗansa ba irin sauran yara bane, sannan shima ya goyi bayan ɗan nasa wato Aarav dangane da wannan zurfin tunani da yayi.
Akshey Kumar dai ya kasance ya kanyi fim kamar guda 3 a cikin sharara guda inda yayi fina-funai da dama a tarihi da masana’antar Bollywood bazata taɓa mantawa da shi ba.