Ƙarancin Man Fetur a hankali yana fuskantar Damaturu da sauran sassan Jahar Yobe, inda ake cigaba da dogon layi a gidajen mai, musamman inda keda man fetur ɗin.
Majiyar Jaridar Dimokuraɗiyya ta bayyana cewa gidajen man fetur da dama sun kulle a garin Yobe, sakamakon Ƙarancin Man fetur.
Inusa Mamman Mohammed mai tuƙa taxi, wanda bayan ya shafe awanni 5, ya bayyana damuwa akan yadda ya sayi man fetur akan farashi Naira 175.
KARANTA WANNAN LABARIN: Wata Sabuwa: IPOB ta baiwa Uzodinma wa’adi ya sako mata mambobin ta
“Bamu san mike faruwa ba a ƙasar nan, kuma babu wanda ke cewa komai game da ƙarancin Man Fetur,” inji shi.
Yayi kira ga Gwamnatin Tarayya da sauran masu ruwa da tsaki a ma’aikatar man fetur da su kawo ɗauki akan ƴan Najeriya, wanda suka dogara akan amfani da Man Fetur domin gudanar da harkokin su.
Wani Mazauni Mohammed Musa yace ya kasance akan layi a gidan man fetur na NNPC tun ƙarfe 5 na safe, amma sai ƙarfe 11 ya samu, amma a farashin Gwamnati.
Yace dalilin farashi mai sauƙi shiyasa mutane ke ɓata lokacin su akan layin.