Gwamnatin tarayya ta sanar da ɗage zaman da zata da ƙungiyar ƙwadago da kuma gamayyar ƙungiyar ‘yan kasuw zuwa ranar Talata domin tattauna batutuwan da suka shafi tattalin arziƙi.
Ministan Ƙwadago da samar da aikin yi Chris Ngige ya bayyana cewa gwamnatin tarayya taso zama da NLC da TUC da kuma sauran ƙungiyoyi masu zaman kansu domin bayyanawa ‘yan Najeriya dalilin da yasa aka yi ƙarin kuɗin Mai.
Sai dai shugaban ƙungiyar Ƙwadago Ayuba Wabba ya shaidawa manema labarai a ranar juma’a cewa ƙungiyar ba zata halarci taron ba saboda ba a aike musu da gayyata akan lokaci ba.
https://dimokuradiyya.com.ng/kungiyar-kwadago-za-ta-dauki-mataki-kan-karin-kudin-fetur-da-lantarki/
Ya ƙara da cewa gayyatar tazo ne a ƙurarren lokaci wanda kuma abu ne mai wuya ‘ya’yan ƙungiyar su samu damar halartar tunda kowanensu zai taho daga wurare daban-daban na faɗin ƙasar nan.
Sai dai kuma ana sa ran ƙungiyar Ƙwadagon zata halarci taron biyo bayan ɗage zaman zuwa ranar Talata.
A ranar Asabar ɗin da ta gabata ne ƙungiyar Kwadago tace zata bayyana matsayarta game da ƙarin farashin man fetur da gwamnatin tarayya ta yi.
Ƙungiyar tace a yanzu ba zata fito aiwatar da zanga-zanga ba har sai ta tattauna domin ganin yi abinda ya kamata.