Ƙarya ne Umarnin Buhari ga Ministan Ilmi ya kawo Ƙarshen Yajin Aikin ASUU cikin sati biyu — Fadar Shugaban Ƙasa
Sakamakon taron da Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi a ranar Talata tare da Ma’aikatu da Hukumomin da abin ya shafa don kawo ƙarshen yajin aikin da Ƙungiyoyin jami’o’i ke yi ya kamata ya wuce zato da tunani.
KARANTA WANNAN LABARIN: Ƴan Najeriya Masu zama waje sun fi kowa Hankali, Ilimi a Amurka, Burtaniya – NiDCOM
Abin takaicin shi ne kusan dukkanin Kafafen Yada Labarai suka bari wasu majiyoyi suka canja masu tunani suka yaudare su, wadanda sun kasance ba masu magana da yawun gwamnati ba.
Jaridar Dimokuraɗiyya ta gano Wannan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da Mai Taimakawa Shugaban Ƙasa na musamman akan Kafafen Yaɗa Labaru Garba Shehu ya fitar mai taken “Akan Yajin Aikin Jami’o’i, Gwamnati a shirye take ta kawo karshen sa.
“A yayin taron ko bayan taron babu wani wa’adi da aka baiwa Ministan Ilimi. A yayin taron, Ministan Ilimi ya buƙaci Ministan Kwadago da ya mika tattaunawar don ba shi damar jagoranci tare da kammala abin da ya fara tun farko da Kungiyar Malaman Jami’o’i (ASUU)”.
“Kuma ya yi alƙawarin cewa zai iya samun yarjejeniya cikin ƙanƙanin lokaci mai yuwuwa makonni biyu zuwa uku”
A yayin gudanar da wannan aiki, Ministan zai yi aiki da dukkan Ma’aikatu da Hukumomin da abin ya shafa.
Garba Shehu yace Fadar Shugaban Ƙasa tana da kyakkyawan fata cewa za a iya cimma yarjejeniya a cikin ƙanƙanin lokaci idan duk bangarorin ba su da taurin kai.
“Muna kira ga dukkanin ɓangarorin da su haɗa kai domin kawo karshen yajin aikin.
“A ɓangaren gwamnati kuwa, dukkan ƙofofin a buɗe suke domin tattaunawa da warware batutuwan da suka shafi yajin aikin.
“Muna kira ga kafafen yada labarai da su daina ƙoƙarin yaɗa labaran ƙarya.
Labarun kafofin watsa labaru da aka tsara waɗanda ke neman gabatar da wani abu daban, an alaƙanta su da wasu, a cikin awanni 24 da suka gabata ba su da amfani ko kaɗan.