- Bidiyon wani dan kasar China da ke tuka wata katafariyar motar takalmi a ƙasar Sin ya bar masu amfani da yanar gizo cikin mamaki a shafukan sada zumunta bayan da bidiyan ya yaɗu.
- Hotunan da suka nuna mutumin cikin fahriya yana tuƙa katuwar motar takalmin fata da ta ɗauki hankali sosai.
- Yawancin masu amfani da yanar gizo sun kasa samun abin yi saboda sha’awa, yayin da wasu ke hasashe game da ingancin tsarin sufurin motar.
Wani ɗan kasar China kwanan nan ya mamaye tituna yayin da yake zagayawa cikin garin sanye da katon takalmin mota.
KARANTA WANNAN LABARIN: Wata ‘yar shara a ƙasar waje na samun kusan miliyan ɗaya a duk wata.
Bidiyon da @thiennguyen030913 ya wallafa ya ɗauki hoton wani mutum yana tuka wani katon takalmin mota na fata. Bidiyan na da tsawon mintuna 3.
Mutumin da ba a san ko wanene ba, ya yi amfani da babbar takalmin a kan tituna, da wata tuta da ke kaɗawa a bayan takalmin.
Da yawa ga yan kallo sunyi cirko cirko a lokacin da mutumin ya ajiye takalmin motar tasa a wani wurin ajiye motoci da ke kusa.
Masu wucewa da masu kallo sun kasa tafiya sai dai sun tsaya cak, suna zaro cike da mamaki da ban sha’awa.
Bidiyon ya zama abin mamaki, a wajen mutane, sannan suna musayar ra’ayoyinsu na ban dariya tare da ƙirƙirar kalmomi masu ma’ana a kan faifan bidiyan.
Bidiyon ya samu makallata miliyan 1 tare da wasu ‘yan tsokaci akan TikTok
Ra’ ayoyin da kafar sada zumuntar TikTok ta samu game da wannan bidiyan:
@ffy2x6 ya ce:”Gobe za a tuƙa motar safa ke nan.”
@danielhackman265 ya ce: “Abin ban mamaki hawan motar takalmin Robert Wadlow.”
@castedsmart ya ce: “Ina ɗaya ƙafar ta biyun?
@chrispanayi8 ya ce:” Motar taka ta fata ce ko ta roba ce?”
@brinahjackie5 ya ce: “Ba zan iya daina dariya ba.”
@arashrasuli228 ya yi sharhi: “Takalmina takalmina”
@decemberprince17 ya ce: “Ka yi tunanin idan duk motoci sun canza zuwa irin wannan takalmin motar a kan hanya.”
@glorymelvine yayi sharhi: “Babu wani abu da ba zai yiwu ba a China, China duniya ce”