Babbar kotun yankunan Ingila da Wales a ƙasar Birtaniya ta yanke wa attajiri mai harkar man fetur a Najeriya, Abdulrahman Bashir, mai kamfanin Rahamaniyya Oil & Gas, hukunci wata 10 a gidan kaso.
Kotun ta kuma ci Rahamaniyya tarar fam dubu ɗari biyar (kimanin Naira miliyan 250) saboda ƙin bin umarnin kotu.
Shi kuma manajan kamfanin, Adebowale Aderemi, zai biya tarar fam 10,000, da ya yi daidai da Naira miliyan biyar a kuɗin Najeriya.
A watan Fabrairu, Mai Shari’a Butcher, ya zartar da hukuncin ne bisa ƙin yin biyayya ga umarnin da kotun ta ba shi a kan ƙararsa da kamfanin Sahara Energy Resources ya shigar.
“Dalilin wannan hukunci shi ne, Bashir ya saɓa wa umarnin Mai Shari’a Robin Knowles ranar 1 ga watan Agusta, 2019, da kuma umarnin da Mai Shari’a Justice Bryan ya ba shi a ranar 6 ga watan Satumba, 2019,” inji Butcher.
Umarnin da kotun ta ba Rahamaniyya Oil and Gas Ltd, wadda Bashir ke shugabanta, shi ne, ya bayar da man gas adadin Metric tonnes 6,400.69 ga kamfanin Sahara Energy Resource Ltd.
Kotun kuma ta nuna yiwuwar za a iya rage hukuncin zuwa wata shida idan ya aiwatar da abun da kotun ta buƙaci ya yi can baya.