Ƙungiyar Ƙwadago ta ƙasa ta shirya tsaf domin shiga yajin-aiki a ranar Litinin mai zuwa 28 ga watan Satumbar da muke, hakan ya biyo bayan watsi da kiran da ƙungiyar ta ga gwamnatin tarayya akan ta janye ƙarin farashin man fetur da kuma kuɗin wutar lantarki da ta yi a baya-bayan nan.
Ƙungiyar ta umarci ‘ya’yanta dake faɗin jihohin ƙasar da su amsa kiranta a ranar 28 ga watan nan.
Ƙungiyar ta yanke hukuncin shiga yajin-aikin ne bayan da masu ruwa da tsaki na ƙungiyar sun yi taron gaggawa tare da samun matsaya akan tafiya yajin-aikin.
A Kano kuwa a jiya Talata ne wasu matasa suka fito domin nuna amincewarsu dangane da ƙarin wutar lantarki da kuma farashin man fetur, sai dai daga bisani jami’an tsaro sun tarwatsa taron masu zanga-zangar.
Idan ba a manta ba ko a ranar Larabar da ta gabata sai da ƙungiyar ta ƙwadago ta ja kunnen gwamantin ƙasar nan dangane da jawo koma baya ga tattalin arziƙin amma gwamnatin tarayyar ta yi kunnen uwar shegu da su.
Da yake tattaunawa da manema labarai shugaban Ƙungiyar na ƙasa, Ayuba Wabba yace yana da kyau gwamnati ta tsaya tayi duba na tsanaki domin kare talakawan ƙasar nan daga cikin mawuyacin hali da suke ciki.
9