Haɗaɗɗiyar Ƙungiyar Matasan Arewa a ranar Laraba tayi Allah wadai ta shirin Gwamnatin Tarayya na cire tallafin Man Fetur, tana mai gargaɗin tattara Mutanen gaba ɗaya yankin domin nuna rashin amincewa da hakan ta hanyar gudanar da zanga-zanga.
CNG tace shirin Gwamanati na ƙara farashin litar man fetur zuwa Naira 340 yana cigaba da haifar da maganganu marasa daɗi ga ƴan Najeriya, da Ƙungiyoyin Fararen Hula.
KARANTA WANNAN LABARIN: Gwamnatin Tarayya Zata Siyar Da Koguna 12 Ga Yan Kasuwa Don Samin Kudaden Shiga
Dayake jawabi ga Manema Labaru a Gombe a ƙarshen taron masu ruwa da tsaki na Arewa maso Gabas wanda ƙungiyar ta shirya, jami’in shirin Ƙungiyar na Ƙasa wanda ya samu wakilcin Jami’in Ƙungiyar na Jahar Taraba Ibrahim Mohammed ya nuna ɓaci ransa akan shirin ƙara kuɗaɗen litar man fetur.
A cewar sa, alƙawarin biyan diyyar dubu 5,000 a madadin cire tallafin ma fetur ga ƴan Najeriya Miliyan 40 abune da Bama zai yiwu ba, yana mai cewa abune da idan ma za’a biya to zai amfani tsirarun ƴan Najeriya kaɗai.”
Ƙungiyar ta bayyana cewa, zasu miƙa kwafin matsayar da suka cimmawa ga Sarkin Gombe Abubakar Shehu III domin ya duba, duba da cewa sunyi taron ne a Jahar shi.
Mohammed yace “Matsalolin da wahalhalun ƴan Najeriya ba tare da ƙarin kuɗin man fetur ba, ya sanya kayan masarufi sunyi tsada yayi yawa, amma rashin iya mulki a matakin Tarayya da Jahohi da da kuma rashin ƙarfin gwuiwa na Shugabannin Al’umma da na Addini ya sanya sun kasa tashi domin kare martabar Al’ummar yankin dama Najeriya baki ɗaya.