Ƙungiyar ƙaallon ƙafa ta Crystal Palace ta wanke Manchester United a wasan mako na biyu na gasar ajin Firimiya ta ƙasar Ingila a wannan yammaci na Asabar a filin wasa na OldTrafford.
Inda ta wanke ta daci 3 da 1 wanda hakan ke nuni da cewar tunda sanyin safiya Manchester United tayi rashin nasara a wasanta na farko na gasar ajin Firimiya kenan yayin da ita kuwa Crystal Palace tuni ta lashe wasanninta guda biyu data fafata kuma tana da maki 6 kenan.
Mafi yawa ƙungiyoyin ƙwallon ƙafa na ƙasar Ingila kowacce tayi cefane amma ita Manchester United ana ganin kamar batayiba Inda kusa ɗan wasa ɗaya kawai ta sayo daga ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Ajax wato Donny van De Veek kuma shine ya jefa ƙwallon da Manchester taci a yau wato da suka rama guda bayan an dokesu.
Manchester United dai tana da kwantan wasa guda inda a makon farko da aka fara gasar ta Firimiya bata buga wasanta ba inda zata fafata da ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Burnley wanda shima wasa ne mai hatsari a wajen Manchester United.
Akwai ƙalu-bale a wajen mai horas da ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Manchester United wato Ole Gunner Solskjaer ganin yadda ya fara da ƙafar hagu a wasan farko daya fara fafatawa inda kawo yanzu ya kwashe shekaru uku tare da Manchester United.