Sakomakon ayyana zanga-zanga da ƙungiyar Ƙwadago ta NLC da takwarata ta TUC suka shirya yi a ranar Litinin mai zuwa, ƙungiyar gwamnonin ƙasar nan sun shiga ganawar sirri domin kawo ƙarshen matsalar.
Ƙungiyoyin biyu sun shirya gudanar da zanga-zangar ne biyo bayan ƙarin farashin kuɗin man fetur da na wutar lantarki da gwamnatin tarayya tayi a baya bayan nan.
Hakan na cikin wata sanarwar da sakatariyyar ƙungiyar gwamnoni ta fitar mai ɗauke da sa hannun mai magana da yawunta Abdulrazaque Bello Barkindo ya fitar.
Sanarwar ta ce gwamnonin zasu fara tattaunawar na yammacin yau Alhamis don kawo ƙarshen matsalar.
NCL ta ayyana cewa ba gudu ba ja da baya game da shiga yajin-aikin tare da gabatar da zanga-zangar a ranar Litinin mai zuwa.