ƙungiyar ma’aikatan lafiya ta ƙasa JOHESU ta janye yajin-aikin mako guda da ta tsunduma a baya-bayan nan, tare da buƙatar mambobinta da su gaggauta komawa bakin aikinsu.
Hakan na ƙunshe cikin wata sanarwa da ƙungiyar ta fitar a daren jiya Litinin mai ɗauke da sa hannun shugabanta na ƙasa Comrade Bio-bé-ken-tóye Toy Josiah.
Ta cikin sanarwar ƙungiyar ta bayyana cewa ta janye yajin aikin ne duba da cewa gwamnatin tarayya ba ta biya musu buƙatunsu ba, sai dai ta ce nan gaba kaɗan kwamitin zartarwar na ƙungiyar zai yanke hukuncin da za a ɗauka a nan gaba.
https://dimokuradiyya.com.ng/likitoci-na-barazanar-shiga-yajin-aiki-a-ranar-litinin/
Idan ba a manta ba a ranar 13 ga watan nan na Satumba ne ƙungiyar ta tsunduma yajin-aikin gargaɗi na kwanaki bakwai sakamakon rashin biya musu buƙatunsu ciki har da rashin biyan su kuɗaɗen alawus alawus na aikin annobar Korona da Suka yi.
Wannan ba shi ne karo na farko da ƙungiyar ta shiga yajin-aikin ba, ko a makon da ya gabata sai da ta bada gargaɗin zata shiga yajin-aiki.
A watannin da suka gabata ma lokacin da ake tsaka da dokar kulle a sakamakon annobar Korona sai da suka yi kira ga gwamnatin tarayya akan a biya su haƙƙoƙinsu sa suke bi ko su tsunduma yajin-aiki.