Ƙungiyar Mata masu gudanar da sana’ar fim wato, AKAFA, ta shirya gudanar da wani gagarumin taro domin shagalin bikin Sallah.
JARIDAR DIMOKURAƊIYYA ta rawaito cewa Taron shi ne na farko da Matan suka shirya, karkashin kungiyar tun bayan kafuwar ta kusan watanni hudu da suka gabata, kuma zai gudana ne ranar Asabar, 23 ga watan Yuli, 2022.
A yayin taron ana sa ran, dukkan Mata jaruman fim, da wadanda a ke yin harkar fim din da su tun daga farkon kafuwar Masana’antar zuwa yanzu za su halarci wannan taron.
A wata sanarwa da shugabar kungiyar ta kasa Rashida Adamu Abdullahi Mai Sa’a ta fitar ta tabbatar da cewar wannan taron ba a dauke wa duk wata Jaruma da take cikin Masana’antar Kannywwod ba, saboda haka suna gayyatar kowa da kowa.
Sannan duk wata jaruma da take da aure ita ma taron nata ne, don haka suna bukatar ta halarci wajen tare da ya’yanta idan ma akwai masu jikoki to su taho da su, domin taro ne na sada Zumunci da kulla ‘yan’uwanta.
Kamar yadda jaridar Dimokuraɗiyya ta samu labarin sanarwar taron, zai gudana ne a babban dakin taro na Meenah Events Center, dake kan titin Lodge Road, a jihar Kano. Da Misalin Karfe biyu na Rana, a gobe Asabar.