A ranar laraba ne wata babbar kotu a jihar Kaduna ta yanke hukunci kan shari’ar jagoran mazhabar shi’a Sheikh Ibrahim Elzakzaky da mai dakinsa Zeenat, inda ta bada umarnin sakinsu nan take.
Da ma dai ana tuhumar Zakzaky ne dai mai dakin nasa da laifuka takwas da suka hada da tarurruka ba bisa ka’ida ba, da neman tada zaune tsaye da hargitsa lamuran jama’a da dai sauransu.
Sai dai a wata Shari’a da ta gudana a ranar Laraba karkashin nai Shari’a Gideon Kurada ya ce babu wata hujja kuma da ta saura wanda mai shigar da kara ya bayyana dake nuni da laifukan nasu.
Tun a shekara ta 2015 ne dai ake tsare da Sheikh Zakzaky da matarsa Zeenat bayan wasu mabiyansa suka yi arangama da jami’an soji a Zaria.
Da yake tsokaci game da hukuncin kotun, Kakakin Ƙungiyar Shi’a Ibrahim Musa ya ce yanzu ne suka tabbatar cewa an yi wa mutanen biyu adalci.
“A zahirin gaskiya wannan Shari’a ta nuna gaskiya gaskiya ce, domin tun lokacin da ake tsare da su daga 2015 muke kururuwan cewa akwai lauje cikin nadi” Cewar Ibrahim Musa.
“Wannan ba nasara ce kawai ta yan mazhabar shi’a kaɗai ba, nasara ce ta kowa da kowa, kuma hakan ya tabbatar da cewa Mallam Mai gaskiya ne”
Daga bisani kakakin Ƙungiyar ya bukaci gwamnatin tarayya da ta jiha da su martaba umarnin kotun ta hanyar sakin si ba tare da jinkiri ba.