Tsagin Boko Haram na ƙungiyar ta’addanci ta Ansaru ta fara ɗiban ma’aikata a jihar Kaduna, inda take ta raba takardu da goron sallah Lamarin na faruwa ne a wasu ƙauyukan ƙaramar hukumar Birnin Gwari, inda har wasan babur mai ƙayatarwa suka yi wa jama’a da sallah A takardar da suka raba, sun sanar da cewa su ba Boko Haram bane, masu jihadi ne kuma sunnar Annabi suke bi da magabatan farko
Mambobin ƙungiyar ta’addanci ta Ansaru sun fara ɗiban aiki inda suka daukan mazauna yankin ƙaramar hukumar Birnin Gwari ta jihar Kaduna, jaridar Daily Trust ta tattaro.
Ansaru, wani sashin ƙungiyar ta’addanci ne na Boko Haram kuma sun kasance suna cin karensu babu babbaka a kauyukan Birnin Gwari na tsawon shekaru.
KARANTA WANNAN LABARIN: INEC ta fitar da Sanarwa, tace Zata Soke Duk Jam’iyyar da bata yi zaɓen Fidda Gwani nan da wata 1
A ranar Laraba, Daily Trust ta tattaro cewa, mambobin ƙungiyar sun zagaye ƙauyukan Damari, Farin Ruwa, Kwasa Kwasa, Kuyello, Gobirawa har da Tabanni, Kutemeshi da Kazage duk a cikin dabarunsu na daukar jama’a aiki wanda suka fake da shagalin sallah suke.
Wasu mazauna kauyukan da suka zanta da manema labarai sun ce ƴan ta’addan sun rarraba goron Sallah da ya hada da biskit, sun yi wasan mashin wanda ya kayatar da jama’a kuma sun raba takardu da sauran kayayyaki duk daga kungiyar.
Birnin Gwari tana yankin tsakiyar jihar Kaduna ne kuma ‘yan ta’adda sun samu damara ratsa ta inda kudanci da gabashinta ne suka fi shan wuyar.
Abinda takardar da suka raba ta kunsa
Takardar mai shafi biyar mai taken: “Mu ba Boko Haram bane, Ansaru ne” mambobin ƙungiyar sun dinga raba ta a ƙoƙarin su na jan hankalin mazauna yankin su shiga ƙungiyarsu.
Takardar an rubuta ne a tsarin tambayoyi da amsoshinsu. Ta ce “Sunanmu Jama’atul Ansaril Muslimina Fi Biladis Sudan.”
Takardar ta ƙara da ikirarin cewa abinda kungiyar ta fito yi shi ne jihadi inda ta kara da cewa bambancinta da sauran kungiyoyin jihadi shi ne suna bin sunnar Annabi ne da magabata.
Sai dai masana a harkar tsaro sun yi watsi da wannan ikirarin inda suka ce gwamnati, malamai da sarakuna dole su tashi tsaye gudun abinda ya faru a yankin arewa maso gabas.
Sun ce miyagun mutane masu tsawwalawa a addini sun saba amfani da tausasan kalamai wurin yaudarar mutane har su mika wuya kafin su nuna inda suka dosa
Comments 1