Gasar zakarun ƙwallon ƙafa ta nahiyar Afrika gasa ce wadda ba a raba rukuni a zagayen farko, gasa ce wadda sai an buga wasanni guda biyu wato an fitar da wasu ƙungiyoyin ƙwallon ƙafan sannan za a raba rukuni.
Amma kafin afara gasar akwai wasu ƙungiyoyin ƙwallon ƙafan da idan suka nuna bajinta kai tsaye suke samin hutu basai sun buga wasan share fage ba sai dai sujira wasu ƙungiyoyin ƙwallon ƙafan idan sun fito abasu su.
Ga jerin sunayen ƙungiyoyin ƙwallon ƙafan da suka sami tikitin shiga zagayen na gaba tun kafin a fara gasar wato sabuwar kakar wasa ta 2020 zuwa 2021.
Wydad Cassablanca.
Al Ahly.
Espérance Tunis.
TP Mazembe.
Zamalek SC.
Mamelodi Sundowns.
Raja Club Athletic.
Horoya AC.
AS Vita Club.
Primeiro de Agosto