A karon farko, ƙungiyoyin fafutukar kare haƙƙin bil’adama a Nijeriya wadanda suka fito daga Kudancin kasar da kuma arewaci na taro game da yadda za su bayar da gudummawa domin ceto ƙasar daga durƙushewa.
Taron dai na waiwaye kan matsaloli da suka hada da cin hanci da hada fada a tsakanin ƙabilu da mabiya addinin da kuma babakere da aka dade ana yi a gwamnatocin ƙasar da suka gabata.
Taron ya samu halartar ‘ƴan fafutukar kare haƙƙin bil’adama kamar Shattima Yarima da Agba Justin Jalingo da shugaban yaƙi da cin hanci na cacoal Debo adeniran da dai sauransu kamar yadda Bbc suka labarto.