Ƙuri’ar Jin Ra’ayin Kafa Ƙasar Biafra: Kotu ta sake ɗage Shari’ar zuwa 20 ga Oktoba
Babban Kotun Tarayya dake Zaman ta a Abuja ta ɗage Shari’a zuwa 20 ga watan Oktoba na Shekarar 2022, akan ƙarar da Gamayyar Ƙungiyar Ƴan Arewa ta shigar, inda take neman jin makomar Kafa Ƙasar Biafra da sauran waɗanda ke gudanar da fafutukar kafa Ƙasashen su.
Mai Shari’a Inyang Ekwo wanda ya Jagoranci Shari’ar a ranar Juma’a, ya baiwa dukkanin ɓangarorin damar gudanar da ƙuri’ar jin ra’ayi.
KARANTA WANNAN LABARIN:
Da Ɗumi-Ɗuminsa: An ƙona Gidaje, an jima Fasto rauni, bayan zargin ɓatanci ga Annabi SAW a Bauchi
Dayake jawabi bayan ɗage Shari’ar, Lauyan Ƙungiyar Arewa CNG Barista Sufiyanu Gambo Idris yace “abinda Ƙungiyar mai shigar da Ƙara take buƙata shine a baiwa kowane Ɗan Najeriya dama idan yana so ya tsaya Najeriya ko kuma a’a, wanda shine damar su, Kuma muna kira a kan haka.
“Mun gano cewa ta hanyar bada dama ga Dokar Ƴancin Kai ta Afirka, kowane ɗan Afirka yana da damar barin ƙasar da baya so ya zauna, bawai Najeriya kaɗai ba.
“Munga cewa da irin cigaba da aka samu, shine abinda ya dace a baiwa kowane da dama idan yana Son zama Najeriya ko kuma bashi da ra’ayi, Idan zai tsaya a Najeriya shikenan, in Kuma baya so to yaje inda yake so”, Inji shi.
A ɓangaren shi, Lauyan dake neman Kafa Ƙasar Biafra Victor C. Onweremadu yace yankin Kudu maso Gabas ya shigo cikin shari’ar ne, saboda Kotu ta amince yankin ya shigo a Shari’ar.
Yace “Dokar Damar zama Najeriya shi kaɗai ne zai samar da zaman lafiya a Ƙasar. An bar yankin Inyamurai baya sosai. Akwai rashin yin dai-dai ga Inyamurai a Ƙasar nan. Inyamurai na shan wahala sosai
Comments 1